Wolves ta sallami Mick McCarthy

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mick McCarthy

Kungiyar Wolves ta sallami kocinta Mick McCarthy bayan kashin da kungiyar ta sha a hannu Wes Brom da ci biyar da daya a gasar Premier ta Ingila a karshen mako.

McCarthy ya jagoranci kungiyar ne tun daga watan Yulin shekara ta 2006 amma kungiyar ta lashe wasa daya ne cikin goma sha uku da ta buga a jere a baya-baya nan.

"Hukumar gudanarwar kungiyar ta dau wannan mataki ne, saboda rashin nasarorin da kungiyar ta fuskanta wanda ya sa Wolves ta samu maki goma sha hudu cikin wasanni 22 da ta buga a gasar." In ji sanarwar da kungiyar ta fitar.

"Terry Connor zai jagoranci kungiyar na wucin gadi kafin a nada sabon koci."

Sanarwar da kungiyar ta fitar da shi ta kara dacewa: "Muna yiwo Mick McCarthy godiya, saboda gudunmuwar da ya baiwa kuma muna mishi fatan alheri."