Gagarumar tarba ga 'yan wasan Zambia

Hakkin mallakar hoto

'Yan kasar Zambia na can suna bukukuwan lashe gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afrika.

An yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasar gagarumar tarba a Lusaka babban birnin kasar bayan isowar su da kofin da suka lashe.

A daren jiya ne dai 'yan wasan Zambiyar suka doke Kot Divuwa a wasan karshe na gasar.

Wannan dai shine karon farko da suka lashe kofin kwallon kafa na kasashen Africa a tarihinsu.

An yiwa Kot Divuwa kallon wadda zata iya cin kofin tun ma kafun a fara gasar.

Wasan dai sai da ya kai bugun da ga kai sai gola, bayan da aka kammala wasan ana canjaras, duk kuwa da karin lokacin da aka yi.

Wani abu mai kara sosa zuciya a wurin yan kasar ta Zambia shine, an buga wasan karshen ne a birnin Libraville, inda wani hadarin jirgi da ya afku kusan shekaru ashirin da suka wuce, yayi sanadiyar mutuwar baki dayan yan wasan kwallon kafa na kasar ta Zambia a lokacin.

Karin bayani