Huddlestone ba zai buga wasa ba kuma a bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tom Huddlestone

Za'a sake yiwa dan wasan Tottenham Tom Huddlestone aikin tiyata a gwiwarsa kuma ba zai samu taka leda ba a kakar wasanni na bana.

"Ina godiya a sakonninku, ba zan taka leda ba kuma a bana. Za'a yi min tiyata a ranar Juma'a." In ji Huddlestone a shafinsa na Twitter.

"Buri na shine in murmure garau kafin a fara kakar wasanni a bana."

Dan wasan mai shekarun haihuwa 25 ya takawa kungiyarsa leda ne sau hudu saboda raunin da ya samu a karshen shekarar bara.

Tottenham dai a yanzu haka ta ce dan wasan na bukatar karin aiki, domin ta tabbatar da lafiyarsa kafin a fara kakar wasanni na badi.