An fidda Anne Keothavong a gasar Qatar Open

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Anne Keothavong

Agnieszka Radwanska ta fidda 'yar Tennis din Burtaniya Anne Keothavong a wasanni biyu a jere a gasar Qatar Open.

Agnieszka Radwanska 'yar Poland ta fidda a Burtaniyar ce wadda ita ce ta biyu a fagen Tennis din mata da maki 6-1 6-2 a cikin mintuna 63.

A yanzu haka Radwanska za ta fafata ne da 'yar Jamus Jamus Julia Goerges ko kuma Varvara Lepchenko 'yar kasar Amurka a zagaye na gaba.