Da kamar wuya Scholes ya koma Ingila- Ferguson

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paul Scholes

Kocin Manchester United, Alex Ferguson ya ce da kamar wuya Paul Scholes ya koma takawa Ingila leda.

Scholes, mai shekarun haihuwa 37, ya taka rawar gani sosai a wasanni bakwai da ya buga bayan ya dawo taka leda.

Kuma Harry Redknapp, wanda ke cikin wadanda aka ganin zai gaji Capello ya bada shawarar cewa ya kamata dan wasan ya taka leda a gasar cin kofin kasashen Turai.

Scholes dai ya yi murabus a tawagar Ingila ne a shekara ta 2004, yana shekaru 29 da haihuwa.

Dan wasan dai ya ki da dawo takawa Ingila a Lokacin da Capello ya gayyace shi, domin ya bugawa kasar wasa a gasar cin kofin duniya da aka shirya a shekara 2010 a kasar Afrika ta kudu.

Ferguson ya nace cewa yana da kwarin gwiwa dan wasan ba zai dawo taka leda ba, idan aka kara gaiyyyatarsa.