Keshi ya gayyato Yakubu da kaita da Etuhu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samson Siasia bai kira yakubu da Etuhu da kuma Kaita ba a lokacin da yake jagorancin rukunin

Kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya Stephen Keshi ya gayyato Yakubu Ayegbeni da Sani Kaita da kuma Dickson Etuhu cikin tawagar kwallon kasar.

'Yan wasan na cikin jerin sunayen 'yan kwallon da za su takawa Najeriya leda a wasannin share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika da za'a shirya a shekara ta 2013.

Amma dan wasan Chelsea John Obi Mikel bai samu shiga tawagar ba saboda baya samu buga wasa a ko da yaushe a kungiyarsa.

Super Eagles dai za ta fafata ne da Rwanda a ranar 29 ga watan Fabrairu a Kigali.

An fidda Ayegbeni da Kaita da kuma Etuhu ne daga tawagar Super Eagles saboda ba su taka rawar gani ba a gasar cin kofin duniya da aka buga a shekara ta 2010.

Steven Keshi dai ya ce zai garwaya 'yan wasan cikin gida ne da na Turai.

'Yan wasan dake taka leda a Turai:

Mai tsaron gida: Vincent Enyeama (Lille, France)

'Yan wasan baya: Joseph Yobo (Fenerbahce, Turkey), Taiye Taiwo (QPR, England)

Yan wasan tsakiya: Dickson Etuhu (Fulham, England), Sani Kaita (Tavriya, Ukraine), Joel Obi (Inter Milan, Italy), Victor Moses (Wigan, England)

Yan wasan gaba: Ikechukwu Uche (Granada, Spain), Osaze Odemwingie (West Brom, England) Yakubu Ayegbeni (Blackburn Rovers, England), Ahmed Musa (CSKA Moscow, Russia)

'Yan wasan cikin gida:

Chigozie Agbim, Godfrey Oboabona, Juwon Oshaniwa, Gabriel Reuben, Uche Ossai, Sunday Mba, Kalu Uche, Papa Idris, Henry Uche, Osasco Omamo, Obinna Nwachukwu, Izu Azuka, Ejike Uzoenyi, Sunday Emmanuel, Kabir Umar, Kingsley Salami, Uche Oguchi, Okemute Odah, Bartholomew Ibenegbu, Azubuike Egwueke