Mancini ya mayarwa Tevez martani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini ya karyata zargin da Carlos Tevez ya yi, wanda ya ce kocin ya wulakanta shi kamar kare.

Tevez ya yi zargin ne kafin ya dawo City a karon farko cikin watanni uku.

Dan wasan ya soki yadda Mancini ya yi mishi magana, kafin kuma ya ce dan wasan ya ki taka leda a wasan da Bayern Munich ta doke City da ci biyu da nema a gasar zakarun Turai a watan Satumban bara.

"Kwatata ban amince da abun da Carlos ya fadi ba, ban taba wulakanta shi ba." In ji Mancini.

"Bugu da kari shi ne dan wasan da nafi kusanta a koda yaushe."

Tevez, mai shekarun haihuwa 28, ya yi horo ne shi kadai a filin horon kungiyar da ke Carrington a ranar Laraba, bayan an gwada lafiyarsa.

Dan wasan ya dawo Ingila ne daga Argentina a ranar Talata bayan ya yi gudun hijira na tsawon watanni uku.

Tevez dai ya yi asarar kusan fam miliyan goma na albashi da sauran alawus, saboda komawa Argentinan da ya yi.