Ghana na lallashi Asamoah Gyan bayan ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asamoah Gyan

Hukumar kwallon Ghana na tattaunawa da Asamoah Gyan, bayan dan wasan ya ce ya yi murabus daga takawa kasarsa leda.

Hukumar ta ce Gyan ya dauki matakin ne cikin fushi, saboda sukarsa da aka rika yi bayan gasar cin kofin Afrika.

"Hukumar dai na lallashi dan wasan ne, kuma tana bukatar da ya sauya matsayinsa." In ji Sanarwar da Hukumar ta fitar.

Gyan dai ya dauki matakin yin murabus dinne bayan da Zambia ta fidda Ghana a wasan kusa da na karshe a gasar, kuma dan wasan ya barar da fenariti a wasan.

'Yan Ghana da dama ne dai su ka soki dan wasan saboda an fidda kasar daga gasar.

Ghana za ta buga wasu manyan wasanni na kasa da kasa a nan gaba, kuma ma akwai wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 da za a fara a watan Yuni.