Victor Moses ya amince da gayyatar Najeriya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Victor Moses

Agent din dan Najeriya wanda ke takawa kungiyar Wigan leda ya ce dan wasan ya amince da takawa Najeriya leda.

Moses na cikin tawagar Super Eagles da za ta kara da Rwanda a wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika da za'a shirya a shekara ta 2013.

An dai haifi Moses mai shekarun haihuwa 21 ne a Najeriya, amma ya koma Ingila da zama yana shekaru 11 da haihuwa.

Dan wasan dai ya takawa tawagar matasan Ingila leda.

A watan Nuwamban bara dan wasan ya yi watsi da gayyatar da aka yi mishi zuwa tawagar Super Eagles duk da cewa dai Fifa ta bashi damar ya yi hakan.

Dan wasan dai ya fidda rai da takawa babbar tawagar Ingila leda, kuma ya kuduri aniyar taimakawa Najeriya kaiwa gasar cin kofin duniya da za'a shirya a shekarar 2014 a kasar Brazil.

"Ya yi tunani mai zurfi a kai, kuma ya amince dari bisa dari abun da ya ke so ya yi kenan." In ji Agent din dan wasan

"Ina ganin ya sa babu yadda zai yi ya bugawa Ingila wasa, shine kawai ya yanke shawarar dawowa kasar shi ta haihuwa."

Super Eagles za ta yi wasa a Kigali a ranar 29 ga watan Fabrairu da Rwanda.