'Dolene Arsenal ta hada kai'- Arsene Wenger

Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce dolene kungiyar ta hada kai ta ci gaba da fafutuka duk da cewa dai Sunderland ta fidda ta a gasar cin kofin FA.

Sunderland dai ta doke Arsenal ne da ci biyu da nema, kwanaki uku bayan da AC Milan ta lallasa kungiyar da ci hudu da nema a gasar zakarun Turai.

Wannan dai ya nuna karara cewa ga dukkan alamu kungiyar za ta kammala kakar wasan bana, babu kofi ko daya kenan.

"Dolene muyi la'akari da sukar da ake yi mana, kuma ya zama abun da zai karfafa mu, saboda mu fuskanci masu sukar mu." In ji Wenger.

"Yana da wuya mu san matsayin mu a yanzu haka, zamu dai ci gaba da fafutuka."

Wenger wanda ya ke jagorancin Arsenal tun daga shekara ta 1996, ya amince cewa kungiyar za ta kammala kakar wasan bana babu kofi, amma ya ce za ta ci gaba da fafutuka domin ganin ta gama a matsayin na hudu a gasar Premier.

"Zamu maida hankali ne a wasannin mu na gaba mu ga inda zamu kare." In ji Wenger.