Chisora da Haye za su fuskanci shari'a

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan demben biyu dai sun ba hammata iska ne a bainar jama'a a maimakon a filin dembe.

'Yan demben Burtaniya David Haye da Dereck Chisora wanda su ka yi wata dambarwa a birnin Munich na iya fuskantar shari'a a Jamus in ji masu shigar da kara a kasar.

Ana zargin Haye da jiwa wani rauni da gangan laifin da kuma idan an tabbatar za a iya daure shi na tsawon watannin shida zuwa shekaru goma.

Shima dai Chisora ana zarginsa da jima wani rauni saboda ramuwar gayya, wanda kuma idan an tabbatar da laifi za'a daure shi na tsawon shekaru biyar ko kuma a ci tararsa da dauri na tsawon shekara daya.

Haye da Chisora dai sun ba hammata iska ne bayan Vitali Klitschko ya doke Chisora a demben kambun WBC da aka yi a jamus.

'Yan demben sun yi fadan ne a daki ganawa da manema labarai, inda su ka fara da takalan juna.

An dai kama Chisora da mai horadda da shi Don Charles a filin saukar jiragen sama na Munich amma daga baya aka sake su.

Haye dai ya tsere ne daga jamus ne cikin wani jirgin bayan da 'yan sanda su ka neme shi domin su yi mishi tambayoyi.