Ban ga murmurewa ba gada gasar cin kofin duniya- Gyan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asamoah Gyan

Dan wasan Ghana Asamoah Gyan ya amince cewa har yanzu bai gama murmurewa ba daga koma bayan da ya fuskanta a gasar cin kofin duniyar da aka shirya a shekara ta 2010.

Dan wasan dai ya barar da fenaritin da ya kamata ya kai Ghana wasan kusa da na karshe a gasar cin.

Dan wasan dai a yanzu haka ya yi murabus daga tawagar kwallon kasar, bayan ya sake barar da fenariti a wasan kusa dana karshe da Ghana ta buga da Zambia a gasar cin kofin Afrika da aka shirya a bana.

Wannan dai ya jawo mashi suka sosai daga 'yan kasar da dama saboda rashin nasarar da kasar ta fuskanta a gasar.

"Gaskiya a yanzu haka bani da kwarin gwiwa," In ji Gyan.

"Hankali na ya ki kwantawa tun bayan da na barar da fenariti biyu da ya kamata ya taimakawa kasa ta."

"Ban gama murmurewa daga abun da ya fara a gasar cin kofin duniya a shekarar 2010 kuma yanzu ga na shekarar 2012."

Hukumar kwallon Ghana wato GFA ta bayyana cewa tana lallashin dan wasan ne saboda ya sauya matakin da yadauka na yin murabus a harkar kwallon kafa.