Nasri na ganin ya kamata Arsenal ta koyi turjiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan Manchester City, Samir Nasri

Tsohon dan wasan Arsenal wanda ke taka leda a Manchester City, a yanzu haka, wato Samir Nasri ya ce yana ganin ya kamata Arsenal ta rika nuna turjiya idan tana so ta yi nasara.

Dan wasan ya ce dolene kungiyar ta rika lashe wasa komin ta yaya, bai wai sai ta kayatarba.

"A wasu lokutan ba wai sai ka kayatarba, kawai abun da yafi mahimmanci shine kawai kayi nasara."

"Arsenal ta iya taka leda, amma shekaru bakwai kenan babu kofi, kuma gaskiya bai dace ba."

Arsenal dai ta sha kashi a wasanni biyar cikin goma da ta buga, kuma a yanzu haka maki 17 bakwai ne ya rabata da mai jan ragama a gasar Premier wato Manchester City.