Najeriya na neman karin haske daga Fifa

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Shugaban Fifa, Sepp Blatter

Hukumar kula da wasanni a Najeriya na fatan ziyaran da za ta kai gun shugaban Fifa Sepp Blatter a watan Maris, zai warware matsalolin da su ka addabi kwallon kafa a kasar.

A watan Junairu ne wata babbar kotun tarraya da ke Abuja ta ce ta russa Hukumar kula da kwallon kasar wato NFF da kuma Hukumar kula da gasar Premier a kasar wato NPL.

Kotun dai ta bayyana cewa Hukumar NFL da kuma NFA wato sunayen da ake amfani da su baya kadai ne ke da hurumin tafiyar da harkar kwallon kafa a kasar.

NFA dai ta sauya sunanta ne zuwa NFF a shekarar 2009 amma ta gaggara rajistar sunan kumar yadda doka ta tanada.

Wannan dalilan ne dai kuma ya sa dokar kasar ba ta amince da NFF a matsayin hallatacciyar hukumar da ya kamata ta tafiyar da harkar kwallon kafa a kasar.

Hukumar kula da harkar wasanni a Najeriya dai ta shigo cikin lamarin domin warware matsalar, abun da kuma yasa za ta tunkari Fifa domin samun karin haske.

Mai magana da yawun Hukumar, Mista Tony Ohaeri ya tabbatarwa BBC cewa hukumar za ta gana da shugaban Fifa a Zurich a ranar 15 ga watan Maris.