Ya kamata shugabanin Chelsea su nuna mini goyon baya- Villas Boas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya ce ya kamata shugabanin kungiyar sun nuna cewa suna goyon bayan sauyin da yake yi na inganta kungiyar.

Villas Boas wanda ya bayyana haka kafin wasan da kungiyar za ta buga da Napoli a gasar zakarun Turai, ya nace cewa yana sauya al'amura a kungiyar ne domin su rika haskakawa nan gaba.

Villas-Boas ya ce dai shugaban kungiyar Roman Abramovich na goyon bayansa dari bisa dari.

Amma kocin Chelsea din ya ce: "Ya kamata sun bayyana goyon bayan da kansu ba wai a koda yaushe in rika fadi ba."