Za'a yi babban kuskure idan an kori Wenger- Petit

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Petit ya ce Arsene Wenger na fuskantar koma baya a yanzu haka bayan kusan shekaru 16 yana jagorancin Arsenal.

Amma tsohon dan wasan kungiyar na ganin babban kuskure ne idan aka sallami kocin.

Emmanuel Petit ya kara da cewa Wenger ne har wa yau zai iya lallubo hanyoyin da za'a iya amfani da su wajen inganta tawagar kasar.

Ya ce kamata ya yi kungiyar ta ciro kudi domin siyan manyan 'yan wasa da za'a garwaya da matasan Arsenal.

Ga dukkan alamu dai Wenger zai kammala kakar wasan bana bana babu kofi.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar za ta yi shekaru bakwai kenan ba ta lashe kofi ko daya ba.