Ghana ta jinkirta daukar mataki a kan Stevanovic

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tawagar kwallon kafan Ghana

Hukumar kula da kwallon kafa a Ghana ta jirkirta matakin da za ta dauka game da kocin tawagar kwallon kasar, Goran Stevanovic har na tsawon makwanni biyu.

A ranar Laraba ne dai ake kyautata zaton hukumar za ta bayyana matakin da ta dauka game da kocin bayan ta tayi tattaunawa na kwanaki biyu kan rawar da kasar ta taka a gasar cin kofin Afrika da aka kammala.

Amma shugaban hukumar kwallon kasar, Kwesi Nyantakyi ya ce har yanzu hukumar ba ta cimma matsaya ba, game da batun.

"Gaskiya tawagar kasar ba ta taka rawar gani yadda ya kamata ba." In ji Nyantakyi.

Ya ce hukumar za ta kara nazarin domin fitar da cikakken rahoton a kan matakin da za ta dauka game da tawagar kasar.