LuaLua zai dawo tawagar DR Congo- Le Roy

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Claude Le Roy

Kocin DR Congo Claude Le Roy yana fatan dan wasan gaban kasar Lomana LuaLua zai dawo taka leda a tawagar kasar.

Dan wasan wanda ke kungiyar Blackpool ya daina takawa tawagar Leopards, amma daga baya ya sauya ra'ayinsa saboda kocinsa ya bukaci da ya yi hakan.

Kocin ya ce dan wasan zai taka leda a wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika da ksar zata buga da Seychelles a mako mai zuwa.

"LuaLua ya shaida mun cewa zai dawo ne saboda ni, saboda ya rika ya dau matakin takwa tawagar kasar leda." In ji Le Roy.

"Na yi magana da shi, kuma ya amince zai dawo, a yanzu dan wasan na taka rawar gani a Blackpool."