CAS ta kori karar Amos Adamu

amos Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amos Adamu

Kokarin dan Najeriya Amos Adamu na kalubalantar dakatarwar shekaru uku daga shiga harkokin kwallon kafa yaci karo da cikas.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ce ta zargeshi da karbar toshiyar baki da cin hanci da rashawa a kokarin zaben kasar da zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarun 2018 da kuma 2022.

Akan haka ne ya daukaka kara zuwa kotun sauraron kararrakin zabe, amma sai kotun ta kori karar.

Kotun ta ce" nazarin da muka yi ya nuna cewar hukuncin yayi dai dai".

Wasu ma'aikatan jaridar Birtaniya -Sunday Times sun dauki hoton Amos Adamu yana magana dasu akan yadda za a bashi kudi don ya kada kuri'a.

An ga hoton bidiyon Adamu yana maganar a bashi dala miliyon dari takwas don a gina wasu filayen wasa, abinda ya sabawa dokar FIFA.

Karin bayani