Arsenal ta lallasa Spurs da ci 5-2

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Van Persie ya zura kwallo a wasan

Arsenal ta yiwa kungiyar Tottenham Hotspur, dokan kawo wuka a filin Emirates, inda ta lallasa ta da ci biyar da biyu a filin Emirates.

Abu mamaki shine, Spurs ce ta fara zura kwallaye a ragar Arsenal, kafin ta fashe kuma ta daura uku a kai.

Luis Saha ne ya fura zura kwallo a ragar Arsenal ana fara wasan da minti hudu, sannan kuma sai Emmanuel Adebayor ya zura ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kafina a tafi hutun rabin lokaci ne dai kuma Sagna da kuma Robin Van Persie su ka fanshewa Arsenal kwallayen.

Bayan an dawo hutun rabin lokacin ne kuma, Tomas Roscisky ya zura ta uku, sannan kuma Theo Walcot ya zura ta biyar.

A yanzu haka dai Asernal ta na matsayi na hudu kenan a teburin gasar ta Premier.