Liverpool ta lashe kofin Carling

Liverpool ta daga kofi Carling a filin Wembley bayan da ta doke Cardiff da ci uku da biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kungiyoyin biyu sun tashi biyu da biyu ne a wasan kafin a shiga fenarity.

Dan wasan Cadiff mason ne ya fara zura kwallon farko ana minti 19 da wasan bayan kuma an dawo hutun rabin lokaci ne kuma Skertel ya fanshe kwallon.

Kungiyoyin biyu dai sun kammala minti casa'in ne ana daya da daya, abun da kuma ya sa a shiga cikin karin lokaci.

Ana karin lokaci ne Dirk Kuyt ya sanya Liverpool a gaba, amma ana dab da kammala wasan Ben Turner ya fashe kwallon.

Liverpool ta barar da fenarity biyu ta kafar Steven Gerard da Chalie Adam, a yayinda kuma Kenny Miller da Rudy Gestede da kuma Anthony Gerrard suka bararwa Cadiff.