Manchester United ta sha da kyar a hannun Norwich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ryan Giggs

Ryan Giggs ya buga wasansa na dari tara a Manchester United inda ya taimakawa kungiyar a mintin karshe a nasarar da ta yi akan Norwich da ci biyu da daya.

Manchester United na maki biyu ne a bayan City, bayan City din ma ta doke Blackburn Rovers da ci uku da nema a wasan da su ka buga a ranar asabar.

Dan wasan United Paul Scholes ne ya fara zura kwallon farko ana fara wasan a ragar Norwich.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne kuma Grant Holt yan fashe kwallon.

Ana minti karshe ne kuwa Ryan Giggs ya zura kwallon da ya ba Manchester United nasara a wasan.