Mahamadou Diarra zai koma Fulham a karshen kakar wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mahamadou Diarra

Tsohon dan wasan Real Madrid Mahamadou Diarra zai koma kungiyar Fulham da ke kasar Ingila, a karshen kakar wasan bana.

Diarra, wanda Real Madrid ta siye shi a kan fam miliyan 22, ya ci kofin laliga biyu a kakar wasanni hudu da ya yi a kungiyar.

Dan wasan wanda dan asalin Mali ne bai da wata kungiya tun da ya bar Monaco a karshen kakar wasan bara.

Dan wasan zai koma Ingila ne idan an kamalla sa hannu a takardu izini shiga kasa, kuma sai taka leda ne a kungiyar har zuwa shekara ta 2013.