Andy Murray ya doke Michael Berrer a gasar Dubai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray

Dan wasan Tennis din Andy Murray ya sha da kyar a wasan da ya doke Michel Berrer a gasar Tennis ta Dubai.

Murray wanda shine na hudu a duniya a fagen Tennis ya lashe wasan ne da maki 6-3 4-6 6-4 a wasan farko daya buga tun bayan da Novak Djokovic ya doke shi a wasan kusa da na karshe a gasar Australian Open.

Murray dai na buga gasar ne da Novak Djokovic da kuma Roger Federer, amma Rafeal Nadal bai samu halartar gasar ba.

Djokovic wanda ke kare kabunsa a gasar ya fara ne da doke Cedrik-Marcel Stebe a wasansa na farko.