An bukaci Fifa ta bar mata su sa Hijabi

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Shugaban Fifa Sepp Blatter

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Fifa da ta rika bari mata musulmai masu buga kwallo su rika sanya hijabi.

Mai baiwa Sakatare Janar din Majalisar shawara kan harkar wasanni wato Wilfried Lemke ya rubutawa shugaban Fifa Sepp Blatter, wasika game da batun.

Lemke ya rubuta cewa kamata ya yi Fifa ta ba kowannen bangare daman shiga cikin harkar kwallon kafa ba tare da nuna wani banbamci ba.

FIFA dai ta hana sanya hijabi ne a harkar kwallon kafa a shekarar 2007 saboda dalilai na kare lafiya, inda tace huluna ne kawai za'a iya sanya abun da kuma wasu sukayi watsi da shi saboda wuyansu na fitowa.