Scott Parker zai jagoranci Ingila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Scott Parker

Dan wasan Tottenham Scott Parker zai zama kyaftin din Ingila a wasan sada zumuncin da Ingila za a buga da Holland a filin Wembley a ranar Laraba.

Kocin wucin gadi na Ingila, Stuart Pearce ya zabi Parker bisa manyan 'yan wasa kamarsu Steven Gerrard na kungiyar Liverpool da kuma 'yan kungiyar Manchester City James Milner da Joe Hart.

Parker, mai shekarun haihuwa 31, ya buga wasanni 10 wa Ingila, inda ya kara bugawa kasar wasa a watan Nuwanban shekara ta 2003.

Dan wasan ya bugawa Ingila wasa bakwai a shekara ta 2011.

Shine ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Ingila na bara.