Chelsea ta sallami Andre Villas-Bois

Andre Villas-Bois Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Chelsea wanda aka sallama, Andre Villas-Bois

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kori kocinta, Andre Villas-Boas, duk kuwa da cewa bai kai shekara guda yana horar da 'yan wasa a Stamford Bridge ba.

Wannan shawara ta Chelsea dai ta zo ne bayan kashin da kungiyar ta sha a hannun West Brom da ci daya mai ban haushi ranar Asabar.

Haka nan kuma wasanni uku kacal kungiyar ta lashe a cikin wasannin gasar Premier goma sha biyun da ta buga na baya-bayan nan.

A watan Yunin shekarar 2011 ne dai kocin mai shekaru talatin da hudu, dan asalin kasar Portugal, ya kama aiki da kungiyar ta Chelsea.

An nada tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar ta Chelsea, Roberto di Matteo, a matsayin kocin wucin gadi har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Karin bayani