McIlroy ya sha alwashin shiga gaba

Rory McIlroy Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rory McIlroy

Sabon zakaran kwallon golf na duniya, Rory McIlroy, ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da kasancewa a cikin na gaba-gaba a 'yan kwallon golf.

Dan wasan mai shekaru 22 shi ne dan wasa na uku daga Burtaniya da ya zama zakaran kwallon golf a watanni goma sha takwas din da suka gabata, inda ya bi sahun Lee Westwood da Luke Donald.

Tun bayan gasar PGA a watan Agustan bara, McIlroy ya lashe gasanni biyu, ya hau matsayi na biyu sau hudu, sannan ya hau matsayi na uku sau biyu.

Sau daya kacal ya kare ba a cikin 'yan wasa biyar na gaba-gaba ba, lokacin da ya zo na sha daya a Gasar Duniya ta Dubai saboda yana fama da zazzabin Dengue.