Ramires ya tsawaita zamansa a Chelsea

Ramires
Image caption Ramires

Ramires ya tsawaita zamansa a Stamford Bridge zuwa shekarar 2017 bayan ya rattaba hannu a kan wani sabon kwantiragi na shekaru biyar da Chelsea.

Dan wasan tsakiyar dan kasar Brazil, wanda Carlo Ancelotti ya sayo daga Benfica a watan Agustan shekara ta 2010, ya bugawa kungiyar ta Chelsea wasanni har saba'in da daya a dukkan gasannin da ta buga.

Dan wasan mai shekaru ashirin da hudu ya sabunta kwantiragin ne bayan mai kungiyar ta Chelsea ya sallami kocinsa, Andre Villas-Bois, ranar Lahadi.

Ramires ya shaidawa shafin intanet na kulob din cewa: "Ina matukar farin ciki da sabon kwantiragin", sannan ya ce yana "matukar farin ciki da irin goyon bayan da yake samu yayin bugawa kulob din wasa, don haka nake godiya ga Chelsea".

Dan wasan, wanda ke cikin kakar wasanni ta biyu a kulob din, ya sa hannu a kan kwantiragin ne bayan ya buga wasansa na hamsin a Gasar Premier.

Karin bayani