An kafa tarihi da ci 24 a Afirka ta Kudu

'Yan wasan kasa na Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto 1
Image caption 'Yan wasan kasa na Afirka ta Kudu

Kungiyar kwallon kafa ta Mamelodi Sundowns ta kafa tarihi a Afirka ta Kudu bayan ta yi nasarar da ba a taba ganin irin ta ba ranar Lahadi.

Kungiyar ta Sundowns dai ta lallasa takwararta ta Powerlines da ci dai-dai-dai har ashirin da hudu da nema, a gasar cin wani kofi; ta kuma ci kwallaye goma ne a rabin lokaci na farko.

Wannan nasara dai ta sha gaban nasarorin da kungiyar AmaZulu ta Durban ta yi yayin irin wannan gasa a shekarun 1976 da kuma 1986, inda a lokutan biyu ta ci goma sha shida da nema.

Kocin kungiyar, Johan Neeskens, wanda ke cikin 'yan wasan kasar Holland din da suka sha kashi a wasannin karshe na Gasar cin Kofin Kwallon Kafa ta Duniya a shekarun 1974 da 1978, ya yaba da wannan nasar ta 'yan wasansa, yana mai cewa sun nishadantar da 'yan kallo sannan kuma sun yi aikinsu yadda ya kamata.