'Ingila na bukatar sabbin 'yan wasa'

Sven Goran Erikkson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon kocin Ingila, Sven Goran Erikkson

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Sven Goran Erikkson, ya ce idan kungiyar na son taka rawar gani a Gasar cin Kofin Kasashen Turai ta shekarar 2012, to wajibi ne ta samu abin da ya ce mai sauki ne matuka.

"Suna bukatar 'yan wasa masu jini a jika ba wadanda suka gaji ba, ba kuma masu rauni ba.

"In dai daukacin 'yan wasan sabbin jini ne ba wadanda suka gaji ba, to suna da damar ba da mamaki a gasar", in ji Erikkson.

Eriksson, wanda ya ce yanzu haka yana neman aiki ne, ya kuma ce yana matukar kawa zucin sake komawa aikinsa na horar da 'yan wasan na ingila; sai dai ya kara da cewa abu ne mai wuya matuka a sake ba shi mukamin nasa.

Karin bayani