Flamingoes na Najeriya sun tashi zuwa Zambia

Ministan Wasanni na Najeriya, Bolaji ABdullahi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bolaji ABdullahi

Tawagar 'yan wasan kwallon kafar mata 'yan kasa da shekaru goma sha bakwai ta Najeriya, wadda ake yiwa lakabi da Flamingoes, ta tashi zuwa Lusaka, babban birnin kasar Zambia, jiya Laraba, inda za ta buga wasan share fagen zuwa Gasar cin Kofin Duniya na Mata 'yan Kasa da Shekaru 17.

Ranar Asabar za a buga wasan, wanda shi ne zagaye na farko na karawar Najeriya da Zambia a neman gurbin zuwa gasar ta duniya.

Wasan kuma zai zo ne bayan da tawagar ta Flamingoes ta lallasa takwararta ta Kenya da ci biyar ba ko daya, yayinda ita kuma tawagar Zambia ta casa Botswana da ci bakwai da biyu.

Tawagar da ta yi nasara bayan zagaye na biyu na karawar ce za ta wakilci Afirka a Gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya ta Mata 'yan Kasa da Shekaru 17 wadda za a buga a Azerbaijan daga watan Oktoba zuwa na Nuwamba.