'Yan wasan Najeriya za su tafi Amurka horo

Bolaji Abdullahi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan Wasanni na Najeriya, Bolaji Abdullahi

Wadansu ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Najeriya za su tashi zuwa Amurka inda za su ci gaba da horo don shiryawa gasar Olympics ta bana wadda za a gudanar a birnin Landan.

’Yan wasan da za su tafi kasar ta Amurka daga Najeriya su shida za su hadu ne da takwarorinsu da ke can a Atlanta; suna kuma cikin ’yan wasan Najeriya da suka cancanci shiga gasar ta Olympics su talatin da hudu.

Shugaban kwamitin shirye-shiryen zuwa gasar ta Olympics na Najeriya, Alhassan Sale Yakmut, ya shaidawa BBC dalilan da suka sa ’yan wasan za su yi horo a Amurka.

A cewarsa: “[’Yan wasan] da ke Amurka sun fi yawa—yawancin ’yan wasan daliban jami’o’i ne a Amurka—sannan kuma akwai kayan wasa [masu inganci] a can”.

Ya kuma kara da cewa akwai gasannin da ’yan wasan za su shiga wadanda za a yi a kasar ta Amurka a watannin Afrilu da Mayu da Yuni.

“Bayan haka”, in ji shi, “za a dawo Najeriya kuma a yi gasa ta karshe a Calabar a watan Yuni, wadda duk wasu ’yan wasan Najeriya da ke ko ina za su zo, inda za a tantance wadanda suka fi kwazo”.

Karin bayani