Wenger na burin rike matsayi na hudu

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce yana fata juriyar da kugiyarsa ta nuna bayan ta sha kashi a hannun AC Milan zai taimaka mata komawa Gasar cin Kofin Zakarun Turai badi.

'Yan wasan Arsenal din dai sun fice daga gasar ce duk da nasarar da suka yi a kan AC Milan da ci uku da nema ranar Talata, kasancewar a zagayen farko na wasan sun sha kashi da ci hudu ba ko daya: hakan na nufin Arsenal na da ci uku, AC Milan na da ci hudu.

Yanzu dai burin Wenger shi ne kulob din nasa ya kare a matsayi na hudu a teburin Gasar Premier.

"'Yan wasan ba su ji dadi ba [da ficewarsu daga Gasar Zakarun Turai], amma kuma hakan ya kara masu hadin-kai; fatan mu shi ne za mu kammala kakar wasanni ta bana [ta Gasar Premier] cikin nasara", in ji Wenger.

Yanzu haka dai Arsenal na matsayi na hudu ne a kan tebur bayan sun lallasa Tottenham—wadanda ke matsayi na uku—da Liverpool—wadanda ke matsayi na bakwai—yayin da suke da sauran wasanni goma sha daya a gabansu.

Karin bayani