Messi: Dan wasan da ya fi kowa a duniyar kwallo?

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasan Barcelona, Lionel Messi

Wasan da aka buga ranar Laraba tsakanin Barcelona da BayerLeverkusenranar Laraba ne karo na farko da Lionel Messi ya ci kwallaye dai, dai, dai, har biyar a wasa guda tun da ya fara wasan kwallon kafa.

Shi ne kuma karo na farko da wani dan wasa ya ci kwallaye biyar a wasa guda a tarihin Gasar Zakarun Turai.

A baya dai ya taba cin kwallaye hudu a wasa daya (kwallayen da ya ci Arsenal), ya kuma ci kwallaye uku (wadanda ya jefa a ragar Viktoria Plazen), sannan ya ci kwallaye biyu har sau tara a wasa guda a gasar.

Messi ne dan wasa na hudu wanda ya fi cin kwallaye a tarihin Gasar Zakarun Turai da kwallaye arba'in da tara a wasanni sittin da hudu; ya biyo bayan Raul mai kwallaye saba'in da daya, da Ruud van Nistelrooy mai kwallaye hamsin da shida da kuma Thierry Henry mai kwallaye hamsin.

A kakar wasanni ta Gasar Zakarun Turai ta bana, Messi ya ci kwallaye goma sha biyu; wanda ya taba cin kwallaye masu yawa haka shi ne van Nistelrooy a kakar 2002 da 2003 sai kuma shi Messi din kansa a kakar wasanni ta 2010 da 2011.

A kakar wasannin ta bana kwallayen da Messi ya ci sun nunka na sauran 'yan wasan da suka ci kwallaye da yawa; misali Mario Gomez na Bayern Munich ya ci kwallaye shida ne.