BBC navigation

Gasar Olympics: Muhimman bayanai

An sabunta: 9 ga Maris, 2012 - An wallafa a 13:13 GMT

Lambobin zinare da aka lashe a gasar lokacin bazara

1Amurka 929
2Jamus* 400
3Tarayyar Soviet 395
4Burtaniya 207
5Faransa 191
6Italiya 190
7Sauran kasashe 2191
Jumulla 4503

'Yan tseren Amurka LaShawn Merritt, Angelo Taylor, David Neville da kuma Jeremy Wariner suna murnar nasarar da suka samu a tseren mita 400 a gasar Olympics ta 2008 a birnin Beijing.

Lambobin da Gabashi da Yammacin Jamus suka lashe tare

2008

Beijing, China XXIX Olympiad

 1. 204 Kasashe
 2. 10,942 'Yan wasa
 3. 4637 Shirye-shirye

2008 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1China 51
2Amurka 36
3Rasha 23
4Burtaniya 19
5Jamus 16
6Australia 14
7Sauran kasashe 143
Jumulla 302
 • China ta dare saman tebur, duk da cewa tana da karancin lambobi, amma ta lashe zinare da yawa fiye da Amurka.
 • Wurare 37 aka ware domin daukar bakuncin wasannin, ciki har da sabbi 12 da aka gina domin gasar.
 • An samu 'yan kallo mafiya yawa a tarihi inda aka kiyasta cewa mutane biliyan uku da miliyan dari shida ne suka kalli gasar.
 • Dan kasar Amurka Michael Phelps ya kafa tarihi ta hanyar lashe lambobin yabo mafiya yawa a gasar Olympics guda. Ya lashe wasanni takwas a fannin ninkaya.
 • Dan wasan ninkaya na Afrika ta Kudu Natalie du Toit, wanda aka yankewa kafa sakamakon hadarin da ya yi, ya zamo dan wasa na farko mai kafa daya da ya samu damar shiga gasar wasanni ta Olympics tun bayan Oliver Halassy a 1936.

Hagu: He Kexin dauke da lambar zinaren da ta lashe a wasannin Olympics ta 2008.

Dama: Dan wasan ninkaya na Amurka Michael Phelps ya lashe lambar zinare a gasar mita 400 ta maza.

2004

Athens, Girka XXVIII Olympiad

 1. 201 Kasashe
 2. 10,625 'Yan wasa
 3. 4329 Shirye-shirye

2004 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 36
2China 32
3Rasha 28
4Australia 17
5Japan 16
6Jamus 13
7Sauran kasashe 160
Jumulla 302
 • Amurka ce ta sake yin nasara, sai dai China ta sha gaban Rasha. Australia ma ta kara matsawa zuwa mataki na hudu.
 • Chile da China sun lashe lambobin yabo na farko a gasar Tennis.
 • An gudanar da gasar archery a Athens a 2004 a filin wasa na Panathenaic wanda aka yi amfani da shi a gasar Olympics ta 1896.

Hagu: Joanne Hayes na Amurka ta lashe lambar zinare a tseren mita 100 na mata.

Dama: Jun Zhang daga China ta mamaye gasar badminton.

2000

Sydney, Australia XXVII Olympiad

 1. 199 Kasashe
 2. 10,651 'Yan wasa
 3. 4069 Shirye-shirye

2000 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 37
2Rasha 32
3China 28
4Australia 16
5Jamus 13
6Faransa 13
7Sauran kasashe 160
Jumulla 299
 • Amurka da Rasha ne suka zamo kan gaba, yayin da China ke biye musu baya.
 • Koriya ta Arewa da ta Kudu sun shiga filin wasa karkashin tuta guda.
 • Dan wasan Burtaniya Steve Redgrave ya lashe zinare karo na biyar a jere a gasar Olympics.
 • Dan wasan ninkaya na Equatorial Guinea, Eric "the Eel" Moussambani, ya kammala tseren mita 100 akan 112.72 - inda ya ninka adadin wanda ya lashe gasar har sau biyu.
 • An gudanar da gwajin farko domin tantance 'yan wasan da ke amfani da kwayoyin da ke kara kuzari

Hagu: Andrew Hoy na Australia (Azurfa), David O''Connor Amurka (Zinare), Mark Todd New Zealand (Tagulla) bayan sun samu nasara a wasannin tsalle na kwanaki uku.

Dama: Tatyana Lebedeva ta kasar Rasha wacce ta samu lambar azurfa a wasan karshe na tsallen mata

1996

Atlanta, Georgia XXVI Olympiad

 1. 197 Kasashe
 2. 10,318 'Yan wasa
 3. 3512 Shirye-shirye

1996 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 44
2Rasha 26
3Jamus 20
4China 16
5Faransa 15
6Italiya 13
7Sauran kasashe 137
Jumulla 271
 • Amurka da Rasha da Jamus ne suka zamo kan gaba, inda China ta ci gaba da haskakawa.
 • An bude gasar cikin tashin hankali bayan da wasu bama-bamai suka fashe a dandalin wasan inda suka kashe mutane 2 tare da raunata wasu 100.
 • Dukkan kwamitocin shirya gasar Olympics 197 sun samu wakilci a gasar
 • An kara gasar kwallon yashi da hawan duwatsu a jerin wasannin da za a rinka yi a gasar ta Olympics
 • Dan kasar Australia Hubert Raudaschl ya zamo dan wasa na farko da ya halarci gasar Olympics tara.

Hagu: 'Yar wasan ninkaya ta Amurka Beth Botsford tana murnar lambar zinaren da ta lashe a ninkayar mita 100 ta mata tare da takwararta Whitney Hedgepeth.

Dama: Rusha ce ta lashe gasar gymnastics ta maza a gasar ta Atlanta, Georgia

1992

Barcelona, Spain XXV Olympiad

 1. 169 Kasashe
 2. 9,356 'Yan wasa
 3. 2704 Shirye-shirye

1992 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Hadaddiyar tawaga 45
2Amurka 37
3Jamus 33
4China 16
5Cuba 14
6Spain 13
7Sauran kasashe 102
Jumulla 260
 • Tawagar tsohuwar tarayyar Soviet ce ta kasance kan gaba ta hanyar lashe lambobi mafiya yawa, sai kuma Amurka da Jamus. Akalla kasashe 64 ne suka lashe lamba - adadi mafi girma kawo yanzu.
 • Wargajewar tarayyar Soviet da kuma bangon Berlin ya sa ba a samu kasashen da suka kauracewar gasar ba.
 • An kuma karbi tawagar kwallon kwararru ta kwallon kwando. Tawagar kwallon kwando ta Amurka ce ta mamaye gasar sannan kuma ta lashe zinare.
 • Derartu Tulu ta Ethiopia ce ta lashe tseren fanfalaki na mita 10,000, a karshe ta jira abokiyar hamayyarta Elana Meyer, wacce farar fata ce 'yan Afrika ta Kudu. Sun hade hannu tare a wata alama da ke nuna sabon fata na samar da sabuwar nahiyar Afrika.

Hagu: Alexander Kourlovitch ya karbe kambun kilo 205 domin lashe zinare a gasar gwada nauyi ta sama kilo 110.

Dama: Michael Jordan na murna bayan ya lashe zinare tare da tawagar Olympics ta Amurka

1988

Seoul, Koriya XXIV Olympiad

 1. 160 Kasashe
 2. 8,391 'Yan wasa
 3. 2194 Shirye-shirye

1988 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Tarayyar Soviet 55
2Gabashin Jamus 37
3Amurka 36
4Koriya ta Kudu 12
5Yammacin Jamus 11
6Hungary 11
7Sauran kasashe 79
Jumulla 241
 • Tawagar tarayyar Soviet da gabashin Jamus su ne kan gaba.
 • Baya ga Koriya ta Arewa da Cuba da kuma Ethiopia, babu wadanda suka kauracewa gasar.
 • An sake shigar da kwallon kafa a gasar bayan an cimma matsaya da FIFA. Haka kuma an sake dawowa da gasar Tennis.
 • Christa Rothenburger ta zamo 'yar wasa ta farko da ta samu lambar yabo a gasar Olympics ta lokacin hunturu da kuma bazara a shekara guda.

Hagu: Tawagar kwallon kwando ta tarayyar Soviet suna murna bayan sun karbi lambobin zinaren da suka lashe

Dama: Andreas Wecker daga Gabashin Jamus a fagen wasan gymnastics kamar yadda ya saba yi

1984

Los Angeles, Amurka XXIII Olympiad

 1. 140 Kasashe
 2. 6,829 'Yan wasa
 3. 1566 Shirye-shirye

1984 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 83
2Romania 20
3Yammacin Jamus 17
4China 15
5Italiya 14
6Canada 10
7Sauran kasashe 67
Jumulla 226
 • China ta taka rawar gani inda ta kare a mataki na hudu. Amurka ce ta lashe gasar ba hamayya, sai dai Romania ta bayar da mamaki bayan da ta zo ta biyu.
 • Tarayyar Soviet ta yi ramuwar gayya bayan da ta kauracewa gasar tare da wasu kasashe 14. Libya da Iran ma ba su halarci gasar ba.
 • Aka fara gudanar da gudun fanfalaki na mata. A baya an dakatar da gudun bayan da likitoci suka ce zai "sanya mata su rinka tsufa da wuri".
 • An kuma fara gudanar wasannin Rhythmic gymnastics da kuma ninkaya
 • Gasar wasannin Olympics ta farko da aka shirya ba hannun gwamnati, an samu nasara sakamakon kudaden da aka samu ta hanyar kafafen yada labarai da kuma tallace-tallace.

Hagu: Tracy Ruiz wanda ya lashe gasar ninkaya na halartar bikin rufe gasar tare da kocinsa Charlotte Davis

Dama: Aurora Dan na Romania da Chritiane Weber ta Jamus lokacin wasan da suka fafata

1980

Moscow, Rasha XXII Olympiad

 1. 80 Kasashe
 2. 5,179 'Yan wasa
 3. 1115 Shirye-shirye

1980 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Tarayyar Soviet 80
2Gabashin Jamus 47
3Bulgaria 8
4Cuba 8
5Italiya 8
6Hungary 7
7Sauran kasashe 46
Jumulla 204
 • Tarayyar Soviet da Gabashin Jamus ne suka mamaye gasar, yayin da Cuba, Bulgaria da Italy suka lashe lambobin yabo takwas-takwas.
 • Gasar ta farko wacce aka gabatar a kasar da ke bin tsarin kwamunisanci inda Amurka da Yammacin Jamus da Japan da kuma wasu kasashe 62 suka kaurace.
 • Yan matan Zimbabwe da suka lashe zinare a wasan Hockey, an musu kyauta bayan da suka koma gida daga gasar ta 1980.

Hagu: Teofilo Stevenson bayan ya lashe lambar zinare a gasar dambe

Dama: Marita Koch daga Gabashin Jamus na rike da sanda lokacin tseren mita 400

1976

Montreal, Kanada XXI Olympiad

 1. 92 Kasashe
 2. 6,084 'Yan wasa
 3. 1260 Shirye-shirye

1976 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Tarayyar Soviet 49
2Gabashin Jamus 40
3Amurka 34
4Yammacin Jamus 10
5Japan 9
6Poland 7
7Sauran kasashe 49
Jumulla 198
 • Tarayyar Soviet ce ta sake lashe gasar, yayin da Gabashin Jamus ta doke Amurka zuwa mataki na biyu.
 • Kasashen Afrika sun kauracewa gasar domin nuna adawa da sanya New Zealand bayan da 'yan wasanta na Rugby suka ziyarci Afrika ta Kudu karkashin jagorancin 'yan mulkin wariyar launin fata.
 • Bermuda ta zamo kasa mafi karancin yawan al'umma da ta samu lambar yabo a gasar.
 • Birnin Montreal ya kashe dala biliyan daya da rabi wurin shirya gasar - kudaden da basu gama biya ba sai a shekara ta 2006.
 • 'Yar tsalle-tsalle ta kasar Romania mai shekaru 14 Nadia Comaneci ta kasance mutum ta farko da ta ci lamba goma cif-cif. Ta kuma cimma hakan ne a lokuta bakwai daban-dabam

Hagu: John Walker na New Zealand da Frank Clement na Birtaniya a lokacin tseren mita dari takwas

Dama: 'Yar tsalle-tsalle ta Romania Nadia Comaneci tana murna bayan nasarar da ta samu.

1972

Munich, Jamus. XX Olympiad

 1. 121 Kasashe
 2. 7,134 'Yan wasa
 3. 1059 Shirye-shirye

1972 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Tarayyar Soviet 50
2Amurka 33
3Gabashin Jamus 20
4Yammacin Jamus 13
5Japan 13
6Australia 8
7Sauran kasashe 58
Jumulla 195
 • Tarayyar Soviet ta samu kyautukan da suka zarta na kowacce kasa sai Amurka a yayinda Gabashin Jamus ta doke Yammaci inda ta samu kyautar tagulla. 'Yan wasan Soviet sune suka fi haskakawa.
 • Batun kashe mutane 11 daga cikin tawagar Isra'ila a watan Satumba shi ne ya mamaye gasar a wani hari da aka yi wa lakabi Bakar Satumba.
 • Jamhuriyar Rhodesia kasa ce da ba a amince da ita ba a kudancin Afrika, kuma ba a saka ta ba a gasar bisa bukatar kasashen Afrika.
 • An shigar da rantsuwa a hukumance a Olympics, yayinda gasar Archery (harbin kibau) ta dawo gasar
 • 'Yar Birtaniya Lorna Johnstone mai shekaru saba'in da kwanaki biyar, ta zamo mace mafi yawan shekaru dake raye wacce ta fafata a gasar Olympics.

Hagu: Masu tsere suna jiran fara tseren mita 200 a wasan karshe a filin wasa na Olympia dake Munich.

Dama: Ba Amurke Mark Spitz rike da zinare biyar daga cikin bakwai daya lashe a ninkaya a gasar Olympics a Munich.

1968

Birnin Mexico, Mexico XIX Olympiad

 1. 112 Kasashe
 2. 5,516 'Yan wasa
 3. 781 Shirye-shirye

1968 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 45
2Tarayyar Soviet 29
3Japan 11
4Hungary 10
5Gabashin Jamus 9
6Faransa 7
7Sauran kasashe 63
Jumulla 174
 • Manyan kasashe uku sun cigaba a yadda suke, a yayinda Amurka ta shiga gaban Tarayyar Soviet da Japan
 • Wasanni da aka yi cikin yanayin da yafi tsanani a mita 2,239 a sama da dandabaryar kasa. Yanayin kadawar iska na shafar gasar, amma duk da haka an kafa tarihi a tsere na gajeren zango da kuma na gudu.
 • Batun kashe daruruwan daliban dake zanga-zanga adawa da gwamnati shi ne ya mamaye gasar ta Olympics kwanaki goma kafin a soma gasar.
 • A wani mataki mai na saba da siyasa, wasu bakaken Amurkawa 'yan wasa Tommie Smith da John Carlos sun nuna jinjina a matsayinsu na bakake, inda suka karbi kyauta babu takalmi amma sai suka saka bakar safa. Munafarsu ita ce wayar da kai akan talauci tsakanin bakake da kuma nuna wariyar launin fata.
 • An haramta shan kwayoyi masu kara kuzari a gasar Olympics. An dakatar da dan Sweden Hans-Grunner Liljenwall saboda shan giya fiye da kima.

Hagu: Zakaru kuma bakaken fata Tommie Smith da John Carlos suna jinjina irinta bakake.

Dama: Vera Caslavska na Czechoslovakia na fafatawa a gasar dawaki.

1964

Tokyo, Japan XVIII Olympiad

 1. 93 Kasashe
 2. 5,151 'Yan wasa
 3. 678 Shirye-shirye

1964 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 36
2Tarayyar Soviet 30
3Japan 16
4Jamus 10
5Italiya 10
6Hungary 10
7Sauran kasashe 51
Jumulla 163
 • Amurka ta sake komawa ta farko inda Soviet ta koma ta biyu sai Japan ta uku.
 • An dakatar da Afrika ta Kudu daga kwamitin Olympics ta duniya saboda gwamnatin wariyar launin fata. Algeria da Kamaru da kuma Cote d'Iviore sun shiga gasar Olympics a karon farko
 • A shekarar 1964, Japan ta kashe kusan dala biliyon uku a Tokyo saboda Olympics, saboda aikin sake fasalin garin bayan da aka yi girgizar kasa da kuma ta'adi a lokacin yakin duniya na biyu.
 • 'Yar motsa jiki ta tarrayar Soviet Larissa Latynina ta lashe kyautuka shida a karo na uku a jere. Har yanzu ita ce wacce ta fi kowa samun kyautuka a tarihin gasar Olympics inda ta samu 18.

Hagu: Wyomia Tyrus ta Amurka tare da wacce ta wuce a tseren mita 100 na Olympics.

Dama: Dan damben boxing na Amurka Joe Frazier ya doke dan Jamus Hans Huber a gasar Olympics.

1960

Roma, Italiya XVII Olympiad

 1. 83 Kasashe
 2. 5,338 'Yan wasa
 3. 611 Shirye-shirye

1960 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Tarayyar Soviet 43
2Amurka 34
3Italiya 13
4Jamus 12
5Australia 8
6Turkiyya 7
7Sauran kasashe 35
Jumulla 152
 • Kasar China ta cigaba da kauracewa gasar Olympics har zuwa shekarar 1984, a yayinda USSR ta kara shiga gaban Amurka don lashe kyautar zinare sai Italiya ta zama ta uku.
 • An soma yin taken Olympics a hukumance. miliyoyin jama'a kuma sun kalli gasar ta talabijin a fadin duniya.
 • Dan dambe Cassius Clay mai shekaru 18 wanda daga bisani ya zama Muhammad Ali kuma ya kasance zakaran damben boxing na duniya.
 • Dan gudun fanfalaki na Habasha Abebe Bikila ya kasance dan Afrika bakar fata na farko da ya lashe kyautar zinare. Ya yi nasara ne a gasar ta tseren fanfalaki bayan ya yi gudu babu takalmi a kafarsa.

Hagu: Tseren keke a gasar Olympics ta Roma a shekarar 1960.

Dama: Muhammed Ali ya lashe zinare a gasar Olympics a matakin matsakaicin nauyi.

1956

Melbourne, Australia. XVI Olympiad

 1. 72 Kasashe
 2. 3,314 'Yan wasa
 3. 376 Shirye-shirye

1956 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Tarayyar Soviet 37
2Amurka 32
3Australia 13
4Hungary 9
5Italiya 8
6Sweden 8
7Sauran kasashe 46
Jumulla 153
 • Nasarar farko ga USSR, a yayinda ta shiga gaban Amurka da kuma Australia.
 • Kasashen Netherlands da Spain da kuma Switzerland sun kauracewa gasar don nuna adawa da kutsen da Sovieta ta yiwa Hungary. Sauran wadanda basu halarta ba sun hada da China, Iraki, Masar da kuma Lebanon.
 • Wasu daga cikin wasannin an yi su ne a Sweden, saboda sashin lafiya na Australia sun ki amincewa dawaki su shiga cikin kasar saboda saba dokar rigakafi.

Hagu: Zakara dan Soviet Vladmir Kuts (a hagu) ya jagoranci tseren mita 10,000 na Olympics.

Dama: Zakaran Amurka Harold Connolly ya nuna zinarensa bayan ya lashe gasar wurga hamma.

1952

Helsinki, Finland XV Olympiad

 1. 69 Kasashe
 2. 4,955 'Yan wasa
 3. 519 Shirye-shirye

1952 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 40
2Tarayyar Soviet 22
3Hungary 16
4Sweden 12
5Italiya 8
6 Czechoslovakia 7
7Sauran kasashe 44
Jumulla 149
 • Amurka ta zama ta daya, USSR ta biyu sai Hungary ta uku.
 • Yakin cacar baka tsakanin USSR da China shi ne ya mamaye komai, a yayinda take hammaya da kasashen yammacin duniya.
 • Saka wasu shinge ya janyo 'yar Soviet Maria Gorokhovskaya ta kafa tarihi a matsayin matar data fi kowacce samun kyautuka a gasar Olympics daya, inda ta lashe zinare biyu da azurfa biyar.

Hagu: Zakarun Amurka Milton Campbell (Azurfa), Bob Mathias (Zinare), Floyd Simmons (Tagulla).

Dama: 1952: Emil Zatopek (1922-2000) na Czechoslovakia ya samu kyautar zinare a gasar Olympics a 1952 bayan ta lashe tseren mita 10,000.

1948

London, Birtaniya XIV Olympiad

 1. 59 Kasashe
 2. 4,104 'Yan wasa
 3. 390 Shirye-shirye

1948 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 38
2Sweden 16
3Faransa 10
4Hungary 10
5Italiya 8
6Finland 8
7Sauran kasashe 48
Jumulla 138
 • Bayan shafe shekaru 12 ana hutu saboda yakin duniya na biyu, an koma Olympics, amma ba a gayyaci Jamus da Japan ba a yayinda USSR ta kaurace. Amurka ta sake zomawa ta farko a yawan kyautuka.
 • Canza sheka ta siyasa a karon farko: Marie Provaznikova shugabar wasan tsalle-tsallen Czechoslovakia yaki komawa gida, saboda "rashin 'yanci" bayanda aka hada kasar cikin tarayyar Soviet.
 • 'Yar tseren Holland, Franny Blankers-Koen ta lashe zinare har guda hudu.

Hagu: Dan Amurka Robert Mathias ya wurga karfe a gasar Olympics a filin wasa na Wembley.

Dama: Tawagar 'yan kwallon Sweden na sauraron take kasar bayan lashe gasar kwallon Olympics na 1984.

1936

Berlin, Jamus. XI Olympiad

 1. 49 Kasashe
 2. 3,963 'Yan wasa
 3. 331 Shirye-shirye

1936 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Jamus 33
2Amurka 24
3Hungary 10
4Italiya 8
5Finland 7
6Faransa 7
7Sauran kasashe 41
Jumulla 130
 • Jamus ta zama ta daya sai Amurka ta biyu a yayinda Hungary ta zama ta uku.
 • Spain ta kauracewa gasar saboda yakin basasa, Amurka ma ta yi barazanar kauracewa saboda lamuran dake faruwa a Jamus.
 • Jamus mai bin akidar Nazi tana farfadowa a gasar, amma bakin Ba'amurke Jesse Owens ya lashe zinare hudu a gaban Hitler.
 • Gasar ta Berlin ita ce ta farko da aka nuna a talabijin inda aka siyarda tikiti miliyon hudu.
 • Ana shawagi da fitilar Olympics a karon farko.

Hagu: A shekarar 1936, tawagar 'yan wasan Jamus a Budapest.

Dama: Zakaran Amurka 'Jesse' (James Cleveland) Owens a lokacin gasar Olympics a Berlin.

1932

Los Angeles, Amurka. X Olympiad

 1. 37 Kasashe
 2. 1,332 'Yan wasa
 3. 126 Shirye-shirye

1932 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 41
2Italiya 12
3Faransa 10
4Sweden 9
5Japan 7
6Hungary 6
7Sauran kasashe 31
Jumulla 116
 • Amurka ta lashe cikin sauki a yayinda Italiya ta haskaka a karon farko.
 • Sakamakon rage yawan kasafin kudi a Olympics, kashi hamsin cikin dari na yawan 'yan wasan da suka halarci gasar 1928 sune suka halarci na bana.
 • An rage yawan kwanakin gasar Olympics suka koma kwanaki 16. Ba a gudanar da gasar kwallon kafa ba.
 • Gwamnatin Brazil ta kasa tura tawagar ta su 69 zuwa LA saboda rashin kudi, don haka ta zuba a wani jirgin ruwa dauke da Cofee da za su iya sayarwa a Amurka.
 • Gasar farko da aka samu riba, abinda ba a kara samu ba har sai da Los Angeles ta dauki bakuncin gasar a 1984.

Hagu: Jean Shiley na Amurka a lokacin data kafa tarihi gasar tsallen badake.

Dama: Thomas Hampson na Birtaniya ya lashe zinare a yayinda Alexander Wilson na Canada ya zama na biyu a tseren mita 800.

1928

Amsterdam, Netherlands IX Olympiad

 1. 46 Kasashe
 2. 2,883 'Yan wasa
 3. 277 Shirye-shirye

1928 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 22
2Jamus 10
3Finland 8
4Sweden 7
5Italiya 7
6Switzerland 7
7Sauran kasashe 49
Jumulla 110
 • Amurka ta lashe gasar sai kuma Jamus ta zama ta biyu.
 • An bullo da fitilar Olympics sannan kuma aka nunka yawan matan da zasu shiga gasar.
 • 'Yan tseren nahiyar Asiya sun lashe kyauta a karon farko.
 • 'Yar Italiya Luigina Giavotti ta kasance mafi karancin shekaru da ta lashe kyautar azurfa tana da shekaru 11 da kwanaki 302 a duniya.

Hagu: Masu fafatawa a tseren mita 800 na mata a gasar Olympics ta 1928.

Dama: Isoa Fujiki da Takeshi Kuyama, 'yan tawagar Japan suna horo a gasar Olympics ta 1928.

1924

Paris, Faransa. VIII Olympiad

 1. 44 Kasashe
 2. 3,089 'Yan wasa
 3. 135 Shirye-shirye

1924 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 45
2Finland 14
3Faransa 13
4Burtaniya 9
5Italiya 8
6Switzerland 7
7Sauran kasashe 30
Jumulla 126
 • Amurka ta cigaba da haskakawa, amma Finland da Burtaniya da Faransa sun nuna alamun samun nasara.
 • Da farko an shirya yin gasar ce a Amsterdam amma sai aka maida Paris saboda Baron de Coubertin na son ganin gasar a karo na karshe kafin suyi ritaya.
 • Gasar Olympics ta zama ta duniya baki daya inda manema labarai 1000 suke halarta. Sannan an gine makwancin 'yan wasan Olympics a karon farko.
 • Jamus bata halarta ba, amma Latvia da Poland da Uruguay da kuma Ireland sun shiga cikin gasar Olympics.

Hagu: Dan wasan Amurka Harold Osborn (1899-1975) ta samu zinare a tsallake badake a gasar Olympics ta Paris.

Dama: Lt Eyres, kyaftin din Devonport a wani wasa tsakaninsu da tawagar Rugby ta Olympics ta Amurka.

1920

Antwerp, Belgium VII Olympiad

 1. 29 Kasashe
 2. 2,626 'Yan wasa
 3. 65 Shirye-shirye

1920 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 41
2Sweden 19
3Burtaniya 15
4Finland 15
5Belgium 14
6Norway 13
7Sauran kasashe 39
Jumulla 156
 • An koma gasar Olympics bayan hutun shekaru takwas sakamakon yakin duniya na farko.
 • Amurka ta shiga gaban kowa, amma Sweden da Burtaniya da Finland da mai masaukin baki sun samu nasara.
 • Alamar gasar Olympics mai dauke da manyan zobe biyar, an kaddamar dasu a hukumance tare da rantsuwar Olympics din.
 • Ba a gayyaci Jamus da Hungary da Turkiya da Austria ba saboda rawar da suka taka a yakin duniya na farko.
 • Dan damben boxing na Amurka Eddie Eagan shi ne kadai wanda ya samu kyautar zinare a gasar Olympics ta bazara da kuma ta hunturu. Sannan kuma ya lashe zinare a gasar da aka yi a 1932.

Hagu: Wasu 'yan Ingila takwas da suka doke 'yan Italiya a gasar Olympics ta Antwerp.

Dama: Suzanne Lenglen ta Faransa na fafatawa a gasar lokacin Olympics na 1920.

1912

Stockholm, Sweden. V Olympiad

 1. 28 Kasashe
 2. 2,407 'Yan wasa
 3. 48 Shirye-shirye

1912 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 25
2Sweden 24
3Burtaniya 10
4Finland 9
5Faransa 7
6Jamus 5
7Sauran kasashe 23
Jumulla 103
 • Amurka ta sake lashe gasar, amma ta wuce Sweden ne da zinare daya tal, yayinda ta lashe lambobi fiye da Amurka.
 • A karon farko an samu mahalarta gasar daga nahiyoyi biyar na duniya a gasar Olympics.
 • An soma amfani da naurar lokacin zamani a karon farko.
 • Kokawar wrestling tsakanin dan Estonia Martin Klein da dan Finland Alfred Asikainen wanda aka shafe sa'o'i 11 da mintuna 40 kafin Klein ya samu nasara.

Hagu: 'Yar wasan Sweden tana shiga tsohon filin wasa a Stockholm

Dama: 'Yan wasan ninkaya na Burtaniya mata su hudu.

1908

London, Burtaniya IV Olympiad

 1. 22 Kasashe
 2. 2,008 'Yan wasa
 3. 37 Shirye-shirye

1908 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Burtaniya 56
2Amurka 23
3Sweden 8
4Faransa 5
5Jamus 3
6Hungary 3
7Sauran kasashe 12
Jumulla 110
 • Gasar ta samu karbuwa a kasashen duniya. Mai masaukin baki, Burtaniya ce ta zama ta farko
 • An gaggauta shirya gasar Olympics karo na hudu a London, a yayinda Italiya ta fice saboda matsala a Vesuvius.
 • An bullo da batun tutocin kasashe a gasar Olympics.
 • Abinda Pierre de Coubertin ya kirkiro da taken Olympics wanda yace"Abu mafi mahimanci a rayuwa shi ne fice ba wai fada ba, ba kawai a samu nasara ba, amma a nuna hammaya da kyau".
 • Australia da New Zealand sun shiga gasar a matsayin Australasia.

Hagu: Wyndham Halswelle ta lashe tseren mita 400

Dama: Wasu masu wasan motsa jiki

1904

St.Louis, Amurka III Olympiad

 1. 12 Kasashe
 2. 651 'Yan wasa
 3. 6 Shirye-shirye

1904 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 78
2Jamus 4
3Cuba 4
4Canada 4
5Hungary 2
6Burtaniya 1
7Sauran kasashe 3
Jumulla 96
 • Amurka ta haskaka a wasanni 42, ciki hadda na tsalle-tsalle.
 • An bullo da bada kyautar Zinare, Azurfa da kuma Tagulla.
 • Dan Amurka Goerge Eyser ya samu kyautuka shida duk da cewar yana da rauni a kafa.
 • An dakatar da Fred Lorz saboda kokarin yin zamba a gudun fanfalaki ta hanyar shiga mota.

Hagu: Masu fafatawa zasu soma karawa a tseren mita 400

Dama: Soma tsere mai dogon zango a filin Francis, Jami'ar Washington a St.Louis

1900

Paris, Faransa II Olympiad

 1. 24 Kasashe
 2. 997 'Yan wasa
 3. 22 Shirye-shirye

1900 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Faransa 26
2Amurka 19
3Burtaniya 15
4Tawagar gamayya 6
5Switzerland 6
6Belgium 5
7Sauran kasashe 13
Jumulla 90
 • Bayan da ta gabatar da 'yan wasa mafi yawa a gasar Olympics ta 1900, Faransa ta samu kyautuka fiye da kowacce kasa.
 • Saboda karancin masu fafatawa a gasa, wasu wasannin na samun halarta mutane masu jinsi daban daban.
 • Dan kwallon zari-ruga na Faransa haifaffen Haiti, Constantin Henriquez de Zubiera shi ne bakar fata na farko da ya fafata a gasar Olympics.

Hagu: Sweden da Denmark sun samu nasara.

Dama: Wasan tsere a cikin teku a bassin de Meulan

1896

Athens, Girka I Olympiad

 1. 14 Kasashe
 2. 241 'Yan wasa
 3. 43 Shirye-shirye

1896 Olympics

Lambar zinaren da kasashe suka lashe

1Amurka 11
2Girka 10
3Jamus 6
4Faransa 5
5Burtaniya 2
6Hungary 2
7Sauran kasashe 7
Jumulla 43
 • Masanin tarihi dan Faransa, Pierre de Coubertin ya farfado da gasar, wacce William Penny Brookes ya kirkiro.
 • Yawancin 'yan wasan sun fito ne daga kasashen Girka da Jamus da Faransa da kuma Birtaniya. Kuma su ne suka fi samun kyautuka.
 • An hana mata shiga gasar. Masu shirya gasar sunce shigar da mata bai dace ba.
 • 'Yan kallo dubu tamanin ne suka halarta ciki har da, Sarki George na farko a Girka

Hagu: 'Yan wasa uku na horon gudun fanfalaki a gasar Olympics ta Athens.

Dama: Dan Girka Spyridon Louis (1873-1940) wanda ya lashe tseren kilomita 40 , tare da Sarki George na farko a Girka lokacin da yake gabda samun nasara a Olympics na Athens.

Hotuna: Getty Images, AP, Reuters

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.