Daga sakamakon gasar guje-guje ta duniya

Muhammed Aman Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan tseren Habasha, Muhammed Aman

A gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, wato World Indoor Athletic Championship wadda ake yi a birnin Santanbul na kasar Turkiya, sakamakon tseren mita 800 na maza ya nuna cewa Muhammad Aman na Habasha ne ya zo farko yayin da Jakub Holusa na Jamhuriyar Czech ya yi na biyu, sannan Andrew Osagie na Burtnaiya ya zo na uku.

A tseren mita 3,000 na maza kuma Bernard Lagat na Amurka ne ya tserewa abokan tserensa, yayinda Augustine Choge na Kenya ya rufa masa baya a matsayi na biyu. Edwin Soi na Kenya ne ya zo na uku.

A tseren mita 60 na mata, kuwa Veronica Campbell ta Jamaica ce farko, Murielle Ahoure ta Ivory Coast ta biyu, yayinda Tianna Madison ta Amurka ta zo ta uku. 'Yar Najeriya Gloria Asumnu ta zo ne a matsayi na shida.

A tseren mita 800 na mata, Pamela Jelimo ta Kenya ce ta yiwa abokan tsrenta fintinkau, Nataliya Lupu ta Ukraine na binta a baya, sannan Erica Moore ta Amurka ta zo ta uku.

A tseren mita 3,000 na mata kuwa Hellen Obiri ta Kenya ce a kan gaba, masu bi mata a matsayi na biyu da na uku kuma su ne Meseret Defar da Gelete Burka na kasar Habasha.

A tseren ya-da-kanin wani na mita dari hudu na mata kuma 'yan tseren Burtaniya ne suka zo farko, sannan 'yan tseren Amurka, sannan na Rasha.

A tseren ya-da-kanin-wani na mita dari hudu na maza ma, 'yan tseren Burtaniya ne suka sha gaban kowa, na Trinidad and Tobago suka biyo bayansu, sannan na Rasha suka zo na uku.