Manchester United ta sha gaban City a tebur

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wayne Rooney

Manchester United ta tsallake Manchester City ta kuma dare saman tebur a Gasar Premier bayan ta lallasa West Bromwich Albion da ci biyu da nema, yayinda ita kuma Manchester City ta sha kashi a hannun Swansea da ci daya mai ban haushi.

Wayne Rooney ne dai ya ciwa Manchester United kwallayenta: ta farko tare da taimakon Javier Hernadez a miniti na talatin da biyar da fara wasa.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kuma, a minti na saba'in, dan wasan West Brom Keith Andrews ya yamutsa Ashley Young, al'amarin da ya sa alkalin wasa ya baiwa Manchester United bugun daga-kai-sai-mai-tsaron gida.

A minti na saba'in da daya kuwa Wayne Rooney ya doka kwallon a ragar West Brom.

Su kuwa 'yan wasan Manchester City zuwansu Swansea bai yi musu dadi ba, don kuwa kashi suka sha da ci daya mai ban haushi, al'amarin da ya sa suka rikito daga matsayi na farko zuwa na biyu a kan tebur.

An dai tafi hutun rabin lokaci ba ci, amma bayan an dawo, a minti na tamanin da biyu Wayne Routledge ya dago kwallo zuwa kusa da ragar Manchester City, nan take kuwa Luke Moore ya sa kai ya jefa ta cikin ragar.

Wannan dai ya jefa yunkurin Manchester City na lashe Gasar Premier cikin kila-wa-kala.

Karin bayani