Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare —Mancini

Roberto Mancini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya ce ba za a san wanda zai zamo zakaran Gasar Premier ba har sai kulob dinsa ya kara da Manchester United.

Kungiyar ta Mancini ta rikito daga saman tebur ne bayan Swansea ta kidimata da ci daya mai ban haushi - yanzu dai tana bin makwabciyarta, United, a tebur da maki daya

Ranar 30 ga watan Afrilu ne dai City za ta karbi bakuncin United a filin wasa na Etihad, kuma Mancini na ganin wannan wasan ne zai zama 'yar manuniya.

"Ina ganin muna da dimbin kuzarin da za mu iya sake komawa saman tebur—ina ganin ba za a san maci tuwo a wannan gasar ba sai ya rage wasanni uku a kammala", in ji Mancini.

Yayin da City ke shan kashi a hannun Swansea ranar Lahadi ne United ta sha gabanta a tebur bayan da United din ta lallasa West Bromwich Albion da ci biyu ba ko daya.

Sai dai Mancini ya ce rikitowar kulob din nasa bai dame shi ba tun da akwai sauran wasanni goma nan gaba.

Ya kuma ce yana da kwarin gwiwa City za ta lashe Gasar Premier a karo na farko a shekaru arba'in da hudu.