Rosicky ya sabunta kwantiraginsa

Tomas Rosicky Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal, Tomas Rosicky

Dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal, Tomas Rosicky, ya sa hannu a kan wani sabon kwantiragi da kulob din bayan da ya ci kwallaye biyu a wasanni uku.

BBC ta samu rahotannin da ke nuna cewa kyaftin din na Jamhuriyar Czech ya amince da kwantiragin na shekara biyu.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce: "A koda yaushe yadda Tomas ke taka leda na burge ni, kuma ina farin ciki da ya amince ya sadaukar da lokacinsa ga wannan kungiya tamu".

Shi kuma Rosicky cewa ya yi: "Tun bayan zuwa na Arsenal shekaru biyar da suka wuce, ji nake kamar a gida nake".

Karin bayani