Peterson ya zargi Amir Khan da nuna gadara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Lamont Peterson da Amir Khan

Peterson ya zargi Amir Khan da nuna gadara

Lamont Peterson ya zargi Amir Khan da nuna gadara inda yace ya fi iya dambe a wasan farko da suka yi wanda ya janyo cece-kuce.

Khan dai yace zai samu nasara a dambe da za su sake yi a Las Vegas kuma Peterson bai taka wata rawar azo-agani ba kamar yadda ya yi a damben karshe a watan Disamba.

''Ya za kuyi tunanin cewa ba zan iya wani abun azo-agani ba kamar yadda nayi a Washington DC sai dai shi kadai zai iya hakan'' a cewarsa.

A ranar goma sha tara na watan Mayu ne za su sake yin dambe kan wanda zai dauki kambun duniya a Mandalay Bay da ke Las Vegas.