Mai yiwuwa Carlos Tevez ya dawo mako mai zuwa

Roberto Mancini da Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roberto Mancini da Carlos Tevez

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya ce mai yiwuwa Carlos Tevez ya shiga cikin babbar tawagar 'yan wasan kungiyar a wasan da za ta buga da Chelsea a mako mai zuwa.

"Za mu duba mu gani nan da mako mai zuwa; komai dai ya dogara ne a kan ko Carlos din a shirye yake, ya kuma danganta da abubuwa da dama", in ji Mancini.

Dan wasan gaban mai shekaru ashirin da takwas da haihuwa ya kasance a benci ne tun bayan da aka zarge shi da kin motsa jiki a wasan da kungiyar ta sha kashi a hannun Bayern Munich a Gasar Zakarun Turai a watan Satumba.

Sai dai a 'yan kwanakin nan ya buga wasanni biyu a tawagar kungiyar ta biyu bayan ya nemi afuwa daga kungiyar da magoya bayanta.

Karin bayani