Djokovic ya yi nisa a gasar Indian Wells

Image caption Novak Djokovic

Zakaran bara a gasar tennis ta Indian Wells, Novak Djokovic, ya tsallake zagaye na hudu a Gasar Indian Wells bayan ya doke Kevin Anderson na kasar Afrika ta kudu da ci 6-2 6-3.

Dan wasan na daya a duniya wanda ya doke Rafeal Nadal na kasar Spain a wasan karshe a bara ya samu nasara ne a cikin sa'a guda da minti talatin da bawai

Djokovic dai na neman kambu na uku a wasan tennis na BNP Paribas

"Wannan daya ne daga cikin gasannin da nake samun nasara sosai; ina matukar kaunar sake dawowa hamada", in ji Djokovic.