Mai yiwuwa Berbatov ya bar Manchester United

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dimitar Berbatov

Akwai yiwuwar Dimitar Berbatov zai bar kungiyar Manchester United a karshen kakar wasannin bana, a cewar kocin kungiyar, Sir Alex Ferguson.

Kocin ya tabbatar da cewa dan wasan gaban na son ya kasance cikin tawagar dake taka leda a koda yaushe, abin da ba zai iya samu ba a Manchester United.

Berbatov ya taka leda a wasanni biyar ne kawai na gasar Premier a kakar bana.

''A matsayinsa na dan shekaru talatin da daya yana son ya kasance cikin tawagar dake taka leda", in ji Ferguson, wanda ya kara da cewa, "Wannan wani abu ne mai wuya na amince da shi; akwai yiwuwar zai fara neman wata kungiyar".

Berbatov ya rattaba hannu ne a kan yarjejeniyar bugawa Manchester United a watan Satumban shekerar 2008 daga kungiyar Tottenham a kan kudi fiye da fam miliyan talatin.

Ya ci kwallaye goma sha hudu a karkar wasannin farko da ya fara taka leda a kungiyar kuma ya buga kwallo a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai, inda kungiyar ta sha kashi a hannun Barcelona.