Lord Goldsmith ya nuna damuwa kan FIFA

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Shugaban kungiyar FIFA Sepp Blatter

Tsohon Antoni Janar na Burtaniya, Lord Goldsmith, ya shaidawa BBC cewa ya damu game da yadda Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, ke gudanar da bincike bisa zargin magudi da muna-muna a kamfen Gasar cin Kofin Duniya ta shekarun 2018 da 2022.

Goldsmith mamba ne a wani kwamiti mai zaman kansa da hukumar ta FIFA ta kafa a bara domin ya lalubo hanyoyin yiwa hukumar ta FIFA garambawul, bayan jerin zargin badakalar da suka kunno kai.

''Mun dauki lokaci sosai muna yin nazari a kan zarge-zargen game da ayyukan aikata ba-daidai ba a baya, ciki har da yadda ake zabar kasashen da za su karbi bakuncin Gasar Kofin Duniya," in ji Lord GoldSmith.

Ya kara da cewa: ''Mun damu a kan wadansu abubuwa biyu - muna bukatar wani tsari nan gaba da zai rinka sa ido a wurare da dama''.

A shekarar 2010 hukumar ta FIFA ta kori wadansu mambobinta biyu bayan binciken da ta gudanar a kan zargin da ake yi musu na karbar kudi domin nuna goyon baya ga kasashen da ke neman daukar bakuncin gasar ta shekarar 2018.