Sai karshen kaka Mancini zai san matsayinsa

Roberto Mancini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Jami'an Manchester City sun jinkirta tattaunawa a kan makomar kocin kungiyar, Roberto Mancini, har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Tun a watan Disamban da ya gabata ne dai Mancini ya bayyanawa jami'an kungiyar cewa a shirye yake ya tattauna da su dangane da tsawaita kwantiraginsa.

Kwantiragin kocin na City, wanda ya sa hannu a kwanriragin shekara uku da rabi lokacin da ya maye gurbin Mark Hughes a watan Disamban 2009, zai kare ne a watan Yunin shekara ta 2013.

Wasu majiyoyi sun ce sai a karshen kakar wasannin masu kungiyar ta Manchester City za su yanke shawara a kan makomar Mancini, lokacin da za su tantance kokarin da kungiyar gaba daya ta yi.

Tun lokacin da Mancini ya jagoranci kungiyar ta lashe Kofin Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila a watan Mayun bara—kofinsu na farko a shekaru talatin da biyar—aka zaci manyan jami'an kungiyar za su tsawaita kwantiragin nasa, wanda ya kai fam miliyan uku da rabi, amma ba su samu damar yin hakan ba.

Karin bayani