Fifa ta yi murna da warware 'matsalar' Najeriya

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya Fifa ta ce ta samu kwarin gwuiwa da yadda aka warware rikicin da ya dabaibaye harkar kwallon kafa a Najeriya.

Shugaban hukumar Sepp Blatter ne ya bayyana hakan a ganawar da ya yi a birnin Zurich, da wata tawagar jami'an Najeriya karkashin jagorancin Ministan wasannin Najeriya Bolaji Abdullahi da kuma shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya Aminu Maigari.

Hakan kuma ya biyo bayan rahotannin da suka bayyana cewa an janye kararrakin da aka kai hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriyar ana kalubalantar zaben shugabanninta.

"Muna farin cikin cewa an warware wannan matsalar. A yanzu za mu mayar da hankali a kan ci gaban kwallon kafa a Najeriya. In ji Blatter

A watan Janairun da ya gabata, harkar kwallon kafa ta shiga rudani a Najeriya inda wata babbar kotu ta rusa shugabannin hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya da kuma hukumar kula da gasar lig-lig ta Najeriya.

Karin bayani