Button ya yi zarra a bude Australian Grand Prix

Jenson Button Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jenson Button

Direban McLaren Jenson Button ya yi zarra a lokacin bude gasar tseren motoci ta Australian Grand Prix, yayinda abokin tserensa wanda suke kungiya daya, Lewis Hamilton, ya yi na uku.

Button, wanda ya samu shiga gasar a bayan abokin tsesren nasa, ya sha gaban Hamilton ne tun a kwanar farko, ya kuma yi masa fintinkau.

Hamilton ya sarayar da matsayi na biyu ne ga direban Red Bull, Sebastian Vettel.

Direban Red Bull Mark Webber ne ya zo na hudu, a gaban Fernando Alonso na Ferrari.

Direban Williams, Pastor Maldonado, ya koro gangara don karewa a matsayi na shida, sai motarsa ta kubuce masa a zubin karshe.

Da haka ne Kamui Kobayashi na Sauber ya zo na shida.

Karin bayani