Fabrice Muamba na cikin mawuyacin hali

Fabrice Muamba Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fabrice Muamba kafin ya fadi a wasansu da Tottenham

Har yanzu dan wasan Bolton, Fabrice Muamba, na cikin matsanancin halin rashin lafiya kuma zai ci gaba da kasancewa a dakin 'yan-gobe-da-nisa na asibitin zuciya har zuwa akalla safiyar ranar Litinin.

An garzaya da dan wasan na tsakiya mai shekaru ashirin da uku cibiyar ciwon zuciya ta Asibitin Kirji na Landan ne bayan ciwon zuciya ya kama shi lokacin wasansu da Tottenham ranar Asabar.

Wata sanarwar hadin-gwiwa da ta fito daga kungiyar ta Bolton da kuma asibitin ranar Lahadi ta ce: "Har yanzu Fabrice Muamba yana cikin matsanancin yanayi a dakin 'yan gobe-da-nisa.

"Kamar yadda aka saba yi a irin wannan yanayi, an yi masa allurar barci kuma zai ci gaba da kasancewa a wannan yanayi har zuwa akalla sa'o'i ashirin da hudu".

Sanarwar ta kara da cewa "an tsawaita yunkurin farfado da Fabrice tun daga filin wasan har zuwa asibiti, inda daga bisani zuciyarsa ta fara aiki. Kwararrun likitocin zuciya na ci gaba da sa ido a kan halin da yake ciki".

Kocin Bolton, Owen Coyle, ya ce: "Iyalan Fabrice sun bukace ni in mika godiya ga dukkan mutanen da suka aiko da sakwannin fatan alheri ba kawai magoya bayan Bolton ba, har ma magoya bayan sauran kungoyoyi daga ciki da wajen Ingila".

An dage wasan Bolton da Aston Villa na ranar Talata.