Muamba ya dan fara nuna alamun samun sauki

Fabrice Muamba, bayan ya yanke jiki ya fadi Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Fabrice Muamba, bayan ya yanke jiki ya fadi

Likitocin da ke duba dan wasan Burtaniyan nan wanda zuciyarsa ta buga yayin wani wasa ranar Asabar sun ce ya dan fara nuna alamun samun sauki.

Sai dai kuma sun kara da cewa har yanzu yanayin Fabrice Muamba, wanda dan wasan gaba ne na kungiyar Bolton Wanderers, mai tsanani ne.

Ana kula da Muamba ne a dakin 'yan gobe-da-nisa na Asibitin Kirji na Landan.

Asibitin dai ya ce wani kwararren likitan zuciya wanda ke kallon wasan na ranar Asabar, ya ruga cikin filin don bayar da taimakon farko ga dan wasan, kuma yana cikin kwararrun da ke ci gaba da sa ido a kansa.

Karin bayani